ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran APS na kasar ta Algeria ya ce an sami matattun dabbobin ne a cikin jiragen ruwa guda biyu dauke da alkama ton 27,000 a makon da ya gabata.
Ministan ayyukan noma na kasar Algeriya ya bayyana cewa alkamar ba ta da tsabtar da mutane zasu’a iya ci, don haka an maidasu, kuma kasar za ta bukaci a mayar mata da kudaden sayansu.
Banda haka Abdelhamid Hamdani ministan ayyuykan noma na kasar ta Algeriya ya ce an maida wani jirgin ruwan dauke da ton 33,000 na alkamar daga kasar Canada, shi kuma saboda rashin kawo irin alkamar da ake bukatar kamfanin ya kawo.
342/